Home Labarai Nijeriya za ta kwaso ƴan ƙasar ta 270 daga Amirka

Nijeriya za ta kwaso ƴan ƙasar ta 270 daga Amirka

252
0

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen dawo da kimanin ƴan Nijeriya 270 da suka shirya dawowa gida daga Amirka.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin jakadan Nijeriya a birnin New York mai ɗauke da kwanan watan 3 fa watan Mayu.

Jakadan ya ce an shirya jirgin da zai yi safara ɗaya don kwashe ƴan Nijeriyar daga Amirka a daren ranar Lahadi mai zuwa.

Sanarwar ta ce sama da ƴan Nijeriya 700 ne suk yi rajistar neman a kwaso su, amma dai 270 kaɗai za a iya kwasowa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply