Home Labarai Nijeriya za ta samar da karin kaso 30 na hasken lantarki

Nijeriya za ta samar da karin kaso 30 na hasken lantarki

89
0

Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin Nijeriya na shirin samar da kaso 30 na wutar lantarki a karkashin shirin nan na hanyar sabunta samar da hasken wutar lantarki nan da shekarar 2030.

Onu ya tabbatar da hakan ne a wurin taron kungiyar masu fada a ji a bangaren samar da hasken wutar lantarki da ya gudana a Abuja.

Ya ce tun a lokacin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fara gudanar da ayyukan ta a shekarar 2015 ta kara bunkasa hanyar samar da wutar lantarki da ake samu inda ya kai megawatt 390 duk shekara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply