Home Sabon Labari Nijeriya za ta shiga gasar daga karfe a Mauritius

Nijeriya za ta shiga gasar daga karfe a Mauritius

35
0

Tawagar Nijeriya za ta shiga gasar daga karfe ta Africa da za a fara daga 1 zuwa 8 ga watan Afrilun 2021 a Vacoas ta kasar Mauritius.

Daraktan shirye-shirye na kungiyar masu daga karfe ta Nijeriya Christopher Nwadai ya bayyana cewa gasar za ta zama matakin farko na zuwa gasar ta duniya ta Olympic wanda ake ci gaba da shirye shiryensa tun shekarar da ta gabata.

Nwadai ya bayyana cewa wadanda za su wakilci Nijeriya suna karbar horo na musamman a sansanin bada horo da ke birnin Abuja, a kokarinsu na ganin sun ciwo kyautar da za ta ba su damar zuwa babbar gasar ta duniya.

Masu wakiltar Nijeriya a wasan daga karfen sun hada da mata 6 maza 2.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply