Gwamnatin tarayyar Nijeriya na duba yiwuwar bada tallafin kuɗi ga kafafen yaɗa labaran ƙasar domin tallafa masu a lokaci da kuma bayan halin da ake ciki na Covid-19.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu Lai Mohammed ya bayyana haka a Abuja, yana mai cewa babban bankin ƙasar ya tanadar da wasu kuɗi da za su tabbatar da tallafi ga kafafen yaɗa labaran da za su tabbatar da ayyukansu ko bayan wucewar cutar.
Ya ce ana ci gaba da shigo da ɓangarori da dama, kuma kafafen yaɗa labaran lantarki (electronic media) za su gana da ma’aikatarsa don tattauna yadda za a tallafa masu, kasancewar su ne waɗanda cutar ta fi yi wa illa.
