Home Labarai NIMC ta kama cibiyoyin rajistar ɗan ƙasa na bogi a Kano

NIMC ta kama cibiyoyin rajistar ɗan ƙasa na bogi a Kano

60
0

Hukumar samar da katin shaidar dan kasa ta Nijeriya NIMC, ta tarwatsa wasu haramtattun cibiyoyi da ke rajistar lambar shaidar zama dan kasa a Jihar Kano.

An kama masu tafiyar da cibiyoyin ne a loakcin da jami’an hukumar NIMC suka kai wani hari, tare hannanta wadanda aka kaman ga ‘yansanda domin gudanar da bincike.

Daga cikin kayan da aka kama a cibiyoyin sun hada da takardun buga katin dankasa na NIMC, robobin jabu na buga katin shaida, da sauran wasu takardun NIMC da bai kamata a gansu ko ina ba idan ba ga jami’an hukumar ba.

A cikin wana faifan bidiyon da aka wallafa a shafin twitter na NIMC, jami’in harkokin shari’a na hukumar a Kano, ya ce an gudanar da samamen ne tare da taimakon wata tawaga daga Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply