Home Labarai NIRSAL ya samar da N102bn don zuba jari a harkar noman Nijeriya

NIRSAL ya samar da N102bn don zuba jari a harkar noman Nijeriya

76
0

Kamfanin bunkasa dubarun aikin gona na Nijeriya NIRSAL, ya ce ya samar da Naira biliyan 102 a shekaru hudu da suka wuce, da zai zuba a bangaren ci gaban kasuwancin noma.

 

 

Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a Abuja.

Ya ce an tattara kudaden ne daga farkon kafa kamfanin, ba tare da tallafin gwamnati ko babban bankin Nijeriya ba.

Abdullahi ya ce da wannan ci gaba da kamfanin ya samu, gwamnatin tarayya na da damar bunkasa bangaren da za ta ci moriyar sa.

A wani labarin kuma, kamfanin na NIRSAL, ya kulla wata yarjejeniya da kamfanin Microsoft domin samar da manhajar Azure FarmBeats da za ta taimakawa manoman Nijeriya wajen samar da amfanin gona, rage kashe kudade, tare da bunkasar bangaren.

Abdulhameed, ya ce kamfanin ya zabi manhajar ne saboda za ta fi dacewa bin diddikin harkar noman kasar, wanda wani babban bangare ne da ke taimakawa kamfanin wajen samar da kudaden noma da zuba jari.

Ita dai wannan manhaja ta Azure FarmBeats, na taimakawa wajen tattara bayanan aikin gona, bada hasashen lafiya da yanayin kasar gona, bayanan tsirrai da yawan gonakai ta hanyar yin amfani da hanyoyin tattara bayanai na zamani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply