Home Labarai NNPC ba zai ci gaba da kula da matatun mai ba bayan...

NNPC ba zai ci gaba da kula da matatun mai ba bayan gyara su – Kyari

76
0

Manajan Daraktan kamfanin matatar man fetur ta Nijeriya NNPC Mele Kyari ya ce kamfanin ba shi zai ci gaba da kula da matatun man ƙasar ba da zaran an kammala gyaran su.

Kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun kamfanin Kennie Obateru ya fitar, ya ce Kyari ya faɗi haka ne a lokacin da ake zantawa da shi a gidan wani talabijin a jiya Laraba.

Ya ce da zarar an kammala gyaran su, za a samar da wani kamfani ne daban wanda zai tafiyar da harkokin matatun man.

Gyaran matatun man ƙasar dai ya laƙume biliyoyin nairori tun daga shekarar 1999 amma har yanzu babu guda ɗaya daga cikin huɗun da ke aiki cikakke.

Kyari ya ce abun da ake ƙoƙarin yi kan matatun shi ne a samar da ɓangarori masu zaman kan su da za su zuba jari ta yadda matatun man za su kafu da ƙafafuwan su.

Ya ce saɓanin tsarin da matatun man ke tafiya akai, wannan sabon tsarin zai taimaka wajen ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu a matatun man.

Kasancewar aikin shi ne babban abun da ke gaban Kyari tun bayan naɗa shi a matsayin shugaban kamfanin a shekarar 2019, ya ce aikin zai ci gaba kuma za a kammala gyaran matatun man daga nan zuwa shekarar 2022.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply