Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi NNPC ya samu $378m a wata guda

NNPC ya samu $378m a wata guda

146
0

Kamfanin matatar man fetur na Nijeriya NNPC ya bayyana cewa cikin watan Yunin shekarar nan kaɗai ya samu kuɗaɗe fiye da dalar Amirka milyan 378 ta hanyar fitar da ɗanyen mai da iskar gas zuwa ƙasashen ƙetare.

NNPC ya sanar da hakan ne a cikin wani rahoton kasuwanci da ya fitar na watan Yuni (MFOR) da aka wallafa a ranar Lahadi a Abuja.

Rahoton ya ce tashin farashin man a kasuwar Duniya na ɗaya daga cikin abinda ya taimaka wajen samun waɗannan kuɗaɗe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply