DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKasuwanciNNPCL ya ba da bashin N220bn don gyaran matatun man Nijeriya -...

NNPCL ya ba da bashin N220bn don gyaran matatun man Nijeriya – Rahoto

Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya ce ya bai wa matatun man fetur uku na ƙasar bashin sama da Naira biliyan 220 domin gudanar da ayyukan gyara da sauran buƙatun kuɗi.

Bayanan sun fito ne cikin rahoton kuɗaɗen kamfanin na shekarar 2025, wanda ya nuna cewa matatar mai ta Kaduna ta samu Naira biliyan 77.588.

Rahoton ya ce matatar Fatakwal ta samu Naira 2.58, yayin da ta Warri ta samu Naira biliyan 113.327 daga cikin kuɗin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito NNPCL ta bayyana cewa an yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan wasu kuɗaɗen kwangila, haraji da sauran buƙatun da suka shafi aikin gyare-gyaren na matatun.

Kamfanin ya kuma ce yana da wasu manyan rance da ya bai wa kamfanoninsa, ciki har da Naira biliyan 211.6 ga kamfanin NNPC Energy Services Limited domin ayyukan hako mai da binciken ƙasa.

Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bin NNPCL bashin Naira tiriliyan 11.2, wanda kamfanin ya ce ya shafi kuɗaɗen da gwamnati ke binsu.

NNPCL ta ƙara da cewa tasirin kuɗi na sabbin yarjejeniyoyin da take tattaunawa da wasu kamfanonin China domin tallafa wa matatun mai har yanzu ba a iya tantance shi ba, saboda tattaunawa da bincike kan yarjejeniyoyin na ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata