Daga Abdullahi Garba Jani
Gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha ya sanar da nadin tsohon jagoran ”yan wasan Nijeriya Nwankwo Kanu a matsayin babban mai taimaka ma sa na musamman kan harkokin wasanni.

Gwamna Ihedioha ya ba Kanu wannan mukamin ne a birnin Owerri a lokacin da tsohon dan wasan ya ziyarce shi a gidan gwamnati.

Papiloo kamar yadda ake kiran Kanu, ya yi fice a harkar tamaula a shekarun baya.
Mai shekaru 43, ya taba zama dan wasan kulob din Arsenal na kasar Ingila, Ajax da Inter Milan.
