Home Labarai NYSC ta sanar da ranar buɗe sansanin horo

NYSC ta sanar da ranar buɗe sansanin horo

61
0

Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC ta fitar da jihohin da aka tura matasan, Rukunin B zango na II na shekarar 2020.

Babban Daraktan hukumar Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya bayyana haka a ranar Juma’a, lokacin wani taron wayar da kai da aka shirya wa matasan ta intanet.

Ibrahim ya yi kira ga wadanda abun ya shafa su duba shafin intanet na hukumar NYSC domin ganin jihohin da aka tura su.

Ya kuma ce matasan za su shiga sansanin horaswa ne a ranar 19 ga watan Janairu maimakon 18 ga wata da aka sanar tun da farko.

Ibrahim ya kuma yi gargadin korar duk wani matashin da ya saba ka’idojin kariya daga cutar Covid-19 daga sansanin horaswar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply