DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasaObasanjo ya ziyarci Adeleke bayan samun nasarar zaɓe

Obasanjo ya ziyarci Adeleke bayan samun nasarar zaɓe

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo, ya kai wa Gwamnan Osun Ademola Adeleke ziyarar karfafa gwiwa a gidansa da ke Ede, inda ya taya shi murnar samun nasarar tazarce tare da roƙonsa ya ci gaba da kyakkyawan shugabanci a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da kakakin gwamnan Olawale Rasheed ya fitar a Osogbo da ke cewa tsohon shugaban ƙasar ya kuma yi wa Adeleke addu’ar samun ƙarin nasara a wa’adinsa na gaba.

Obasanjo ya ƙarfafi gwamnan da ya ci gaba da mayar da hankali wajen biyan buƙatun al’ummar Osun da kuma samar musu da romon dimokuraɗiyya.

A nasa ɓangaren, Adeleke ya gode wa Allah da al’ummar jihar Osun, yana mai cewa zai ci gaba da yi musu hidima cikin gaskiya da amana.

Kazalika ya yi alkawarin cewa ba zai taɓa kunyatar da al’ummar Osun da duk masu son dimokuraɗiyya waɗanda suka ba da gudummawa wajen samun wannan nasara ba.

Jami’in da ya jagoranci tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Joshua Ogunwole ya ce jimillar ƙuri’un da aka tabbatar sun inganta sun kai 985,079, wanda daga ciki ne Gwamna Adeleke ya samu ƙuri’u 511,067, shi kuma ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Oyebamiji ya zo na biyu da ƙuri’u 444,815, Najeem Salaam na ADC ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata