Hukumar zaben Nijeriya (INEC) ta sanar da sunan gwamna mai ci Mista Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo.
Mista Obaseki ya lashen zaben gwamnan jihar da yawan kuri’u 307,955, yayin da Mista Ize-Iyamu na jam’iyyar APC ke mara masa baya da yawan kuri’u 223,619.
Tuni dai yan jam’iyyar PDP, magoya bayan gwamna Obaseki suka fara murna kan nasarar ta sa.
Turka-turkar siyasa dai ce dai ta sanya gwamna Obaseki ya sauya sheka daga APC ya koma PDP, ana dab da zaben fidda gwani a jihar.
