Ƙungiyar OK Movement mai goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, ta yi watsi da shirin haɗa ƙungiyar da wata ƙungiyar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin cire wanda ya kafa ta kuma Darakta-Janar, John Ughulu, inda ta ce tsarin ayyukanta na ƙasa ya ginu ne a kan jagorancinsa. Matsayar ta fito ne a cikin wata sanarwa da jagorar ƙungiyar, Lauya Ladipo Johnson, da sakatariyarta, Sadaatu Sani, suka rattabawa hannu a Abuja.
OK Movement ta ƙunshi magoya bayan Obidient Movement da Kwankwasiyya, kuma ta ce za ta ci gaba da kasancewa ƙungiya mai zaman kanta, duk da cewa a shirye take ta yi aiki tare da sauran ƙungiyoyin da ke da manufofi makamancin nata.
Ƙungiyar ta ce duk wani yunƙurin haɗa ta ko shigar da ita cikin wata ƙungiyar siyasa daga waje zai iya kawo cikas ga shirye-shiryen da take gudanarwa tare da raunana tsarin ƙungiyar da ƙarfin da ta samu a matakin ƙasa.
A cikin sanarwar, OK Movement ta ce, “samun ‘yancin kai ba yana nufin ware kai ba ne — muna nan a shirye domin yin aiki tare da ƙungiyoyin da muke da manufa ɗaya da su.”
Lauya Ladipo Johnson ya ce biyayyar mambobin ƙungiyar ba ta mukami ce kawai ba, tana da alaƙa da mutumin da ya kafa ƙungiyar, ya horar da mambobinta tare da jagorantar ayyukanta.
Ya ce idan aka cire Darakta-Janar ɗin ko kuma aka yi watsi da ‘yancin ƙungiyar, wasu mambobin sun nuna cewa ba za su ci gaba da aiki ƙarƙashin sabon tsarin ba.
