Babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Muhammad Adamu ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan za ta kara zage dantse wajen kara inganta aikinta a zaben gwamnan jihar Ondo za a gudanar a watan Octoba mai kamawa.
Muhammadu Adamu ya bayyana hakan ne ga wakilan hadakar kungiyoyin ma’aikata da suka kai masa ziyara a Abuja.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da hada hannu da hukumar zabe ta kasa wato INEC da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe wajen tabbatar da sahihin zabe da kowa zai yi na’am da shi.
