Home Labarai Oshiomhole ke da alhakin rikicin majalisar Edo – PDP

Oshiomhole ke da alhakin rikicin majalisar Edo – PDP

109
0

Jam’iyyar PDP ta zargi tsohon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da jibge jami’an tsaro a majalisar dokokin jihar Edo.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da yake gargaɗin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya dakatar da yinƙurin ƙwace majalisar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ologbondiyan ya ce jibge jami’an tsaro a majalisar juyin mulki ne ga tsarin demokraɗiyyar jihar Edo da kuma haifar da tada zauna tsaye.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taka wa Oshiomhole birki kafin ya kai ga haifar da rikici a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply