Home Labarai Oshiomhole ya soki APC kan sabunta rajista

Oshiomhole ya soki APC kan sabunta rajista

29
0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, ya kalubalanci aikin sabunta rajistar ‘yan jam’iyyar, da APC ke gudanarwa a fadin kasar, yana mai cewa sabunta rajistar ya saba da kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Da yake magana da ‘yan jarida bayan ya gaba sabunta rajisatar tasa, Oshimhole ya ce kamata ya yi APC ta ce tana yin bita ne ko kuma bada damar kara bayanai, ba wai sabunta rajistar ba.

Jigajigan jam’iyyar APC dai, irin su shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun sabunta tasu rajistar.

 

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply