Home Sabon Labari Ozil zai iya barin Arsenal amma… – Arteta

Ozil zai iya barin Arsenal amma… – Arteta

72
0

Mai horaswar Arsenal Mikel Arteta ya ce ɗan wasan tsakiya Mesut Ozil zai iya barin ƙungiyar a watan nan, idan har an samu tayin da ya dace da ɗan wasan da kuma ƙungiyar.

Wakilan Ozil dai na gudanar da ganawa wasu ƙungiyoyi da suka hada da Fenerbahce da DC United, duk da cewa ɗan wasan ya fi son sai ya kai ƙarshen kwantaraginsa a Arsenal.

Ɗan wasan mai shekara 32 wanda bai cikin jerin ƴan wasan da ke bugawa Gunners a dukkan gasar wasannin da take buga wa, duk kuwa da kasancewarsa ɗan wasan da ya fi kowa albashi a ƙungiyar, yana da damar ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyi a wannan watan, kafin ƙarewar kwantaraginsa a ƙarshen kakar bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply