Home Sabon Labari Pantami ya rufe rajistar NIN a shelkwatar hukumar NIMC

Pantami ya rufe rajistar NIN a shelkwatar hukumar NIMC

73
0

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da rufe babbar shelkwatar hukumar samar da shaidar katin zama dan Kasa ta (NIMC) ga wadanda ke zuwa domin yin rajista a shelkwatar da ke Abuja.

Jami’in yada labarai na hukumar NIMC, Mista Kayode Adegoke ne ya bayyana hakan, inda ya ce umurnin ya zo ne daga Ministan Sadarwa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami.

Adegoke ya ce ministan ya kuma bukaci a sake bude wasu sabbin cibiyoyi har guda 20 a cikin kwaryar birnin tarayya (FCT) domin su cigaba da gudanar aikin samar da shaidar ta NIN cikin sauki ga wadanda suke da bukata daga ranar Litinin, 18 ga Janairu 2021.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply