Shugaban cocin Roman Catholic Fafaroma Francis ya nuna takaicinsa game da hukuncin da Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyib Erdogan ya dauka na mayar da dadadden ginin nan na adana kayan tarihi Hagia Sophia zuwa masallaci.
Fafaroman ya ce ginin na Hagia Sophia wuri ne da ya kasance inda kiristoci ke bauta kimanin shekaru 1,500 da suka gabata kafin sarakunan Daular Ottoman su kafa mulki.
Wata kotun kasar ce dai ta soke sunan ginin daga matsayin wurin adana kayan tarihi, ta kuma bayyana cewa ta haramta duk wani abu da za a gudanar a wannan wuri idan ba masallaci ne ba.
Tuni dai Shugaban Erdogan ya bayyana cewa za a gabatar da sallar farko a Hagia Sophia ranar 24 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.
