Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya kwaɓi tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar kan iƙirarin sa ga jam’iyyar PDP.
Atiku wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2019, ya faɗa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, cewa PDP ta zama abar kwatance kan tsarinta da bin doka, inda ya yi kiran ganin hakan ya ɗore.
To sai dai a martaninsa, Lamiɗo ya ce tuni PDP ta rasa ƙimar da za ta iya yin wannan iƙirarin, yana mai cewa har sai an duba irin rawar da kowa ke takawa sannan za a gano irin raunin wannan iƙirari na Atiku.
Dukkan su dai, ana ganin suna daga cikin na gaba-gaba a jerin waɗanda za su nemi takarar shugaban ƙasa a 2023.
