Home Labarai PDP na neman darewa gida biyu a Katsina

PDP na neman darewa gida biyu a Katsina

463
0

Jam’iyyar PDP a jihar Katsina na neman darewa gida biyu a dai-dai lokacin da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka koma gefe suka kafa “PDP A Gyara” a jihar.

A taron manema labarai a Katsina, jagoran sabuwar tafiyar jam’iyyar Lawal Rufa’i Safana yace babban burinsu shi ne jam’iyyar ta dinke dukkanin barakar da ta ke da ita domin ganin ta lashe babban zabe mai zuwa na 2023.

Lawal Rufa’i Safana Wanda shi ne tsohon babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu na jihar Katsina a zamanin mulkin gwamna Shema ya yaba da yadda kotu ta soke zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Katsina, inda yace hakan ya kara ba mutanen kwarin guiwa kan ayyukan sashen shari’a.

Ya tunaso cewa ko a 2015 da jam’iyyar ta fadi zabe, sai da aka kafa wani kwamitin mashawarta da zai taimaka a lalubo bakin zaren warware matsalolin da jam’iyyar ta afka, amma wasu tsiraru daga ciki suka yi gaban kansu domin cika burin wasu tsirarun mutane a ciki.

Yace jam’iyyar ta manta cewa adawa take yi yanzu da take bukatar ta karfafa kafin ta tunkari jam’iyya mai mulki, kan haka ne ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su zo a tafi da su a tafiyar “PDP A Gyara” domin ganin an gudu tare an tsira tare.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply