Home Labarai PDP ta fice daga zaɓen ƙananan hukumomin Kano

PDP ta fice daga zaɓen ƙananan hukumomin Kano

114
0

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ta fice daga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin da za a gudanar a jihar, ranar 16 ga watan Janairun baɗi.

Shugaban kwamitin riƙon jam’iyyar Alhaji Ɗanladi Abdulhamid Kagara ya sanar da haka a lokacin wani taron ƴan jarida da ya gudanar ranar Talata, a Kano.

PDP ta ce bata da ƙwarin guiwar cewa gwamnatin Ganduje da hukumar zaɓen jihar za su yi adalci, a don haka maimakon ɓata lokacinsu, za su yi amfani da damar wajen mayar da hankali kan yadda za su ƙwace mulkin jihar a zaɓen 2023.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply