Home Sabon Labari PDP ta fusata da hukuncin kotu da ya ba shugaba Buhari nasara,...

PDP ta fusata da hukuncin kotu da ya ba shugaba Buhari nasara, za ta daukaka kara

60
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Jaridar Premium Times ta ruwaito daya daga cikin lauyoyin Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Mike Ozekhome ya ce za su kalubalanci hukuncin da kotun sauraren korafe-korafen zaben shugaban kasa ta yanke.

 

A ranar Larabar nan ne kotun ta yanke hukuncin korar karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka shigar, suna kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben 23 ga watan Fabrairu, 2019.

 

Da suke yanke hukuncin, kwamitin alkalai 5 karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Garba, sun kori karar da Atiku Abubakar ya shigar bisa ga abin da suka kira ya gaza kare dukkanin zarge-zargen da ya gabatar. Sai dai Mr Ozekhome ya ce Atiku Abubakar zai kalubalanci wannan hukuncin har zuwa kotun koli.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply