Home Labarai PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa ƴan majalisar Tarayya 7

PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa ƴan majalisar Tarayya 7

33
0

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ta janye dakatarwar da ta yi wa shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya tare da wasu ‘yan majalisar shida a watan Yulin shekarar 2019.

Jam’iyyar ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da kakinta na kasa Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
Ologbondiyan ya ce kwamitin zartaswa na jam’iyyar ya dauki matakin janye dakatarwar ne biyo bayan shawarwarin da kwamitocin da aka kafa kan batutuwan da suka janyo dakatar da ‘yan majalisar suka bayar.
Jam’iyyar ta bukaci ‘yan majalisar su zama masu da’a ga jam’iyyar tare da yin biyya ga umurninta, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply