Home Labarai PDP ta lashe zaɓen cike gurbi na Zamfara

PDP ta lashe zaɓen cike gurbi na Zamfara

90
0

Hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar PDP Ibrahim Tudu a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin da aka gudanar a jihar Zamfara.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen a ranar Laraba, jami’in zaɓen Farfesa Yahaya Tanko na Jami’ar Usmanu Ɗanfodio Sokoto, ya ce Tudu ya samu ƙuri’u 23,874, inda ya kada Ɗan-Kande Bello na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 16,546.

Da yake magana da ƴan jarida bayan faɗin sakamakon zaɓen, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya buƙaci wanda ya lashe zaɓen ya ba maraɗa kunya ta hanyar zama wakili na gari ga jama’a.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply