Home Labarai PDP za ta amshi mulkin jihar Katsina a 2023 – Majigiri

PDP za ta amshi mulkin jihar Katsina a 2023 – Majigiri

148
0

Jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta ce ta shirya tsaf domin amsar mulki daga APC a babban zaben 2023 a jihar.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, shugaban jam’iyyar na jiha, ne ya yi wannan furucin a bayan kammala zaben shugabannin jam’iyyar na jiha da ya gudana a hedikwatar jam’iyyar, Katsina.

Salisu Majigiri, yace irin ayyukan raya kasa da gwamnatin PDP ne ya sa al’ummar jihar Katsina ke mamarin ta dawo.

Ya zayyano ayyuka irinsu jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, asibitin Turai, asibitin kashi (Orthopaedic), gidan gwamnatin jiha da sauransu da yace duk PDP ta yi su.

Majigiri yace yadda babban zaben shugabannin jam’iyyar na jiha ya gudana lami lafiya, wata manuniyace da ke alamta cewa jam’iyyar za ta amshi mulki a 2023.

Babban zaben shugabannin jam’iyyar na jiha ya gudana ne a Litinin din nan, inda aka zabi wadanda za su tafi da ragamar jam’iyyar na shekaru 4 su 39.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply