DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeLabaraiPeter Obi ya bukaci Tinubu ya bayyana takardun karatunsa a fili

Peter Obi ya bukaci Tinubu ya bayyana takardun karatunsa a fili

Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi cikakken bayani tare da fayyace batutuwan da suka shafi takardun karatunsa, musamman bayan ƙoƙarin hana fitar da wasu bayanan kotunan ƙasashen waje da suka shafi tarihin shugaban.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obi ya ce abin da ke faruwa abin kunya ne ga Nijeriya, yana mai cewa batutuwan da suka shafi shugabannin ƙasa kuma suke da muhimmanci ga jama’a bai kamata a ɓoye su ta hanyar amfani da matakan shari’a ba.

Ya ce shugabanci na buƙatar jarumtaka da tawali’u wajen fuskantar abubuwan da suka faru a baya, tare da amincewa da kura-kurai, bayar da bayanai masu gamsarwa idan tambayoyi suka taso, da kuma neman afuwa idan ya zama dole.

Ɗan takarar na jam’iyyar NDC ya jaddada cewa batutuwan da suka shafi takardun karatun firamare da sakandare na shugaban ƙasa suna da muhimmanci, saboda ya kamata a tabbatar da sahihancinsu ba tare da barin su su zama batun da ake gwabzawa a kotu ba.

Obi ya ce ’yan Nijeriya na buƙatar bayani a sarari, sahihi kuma mai iya gamsarwa kan irin waɗannan takardu, musamman ganin cewa an taɓa amfani da su a hukumance a baya.

Ya kuma nuna damuwa kan irin saƙon da takaddamar ke aikawa ga matasan Nijeriya, ciki har da sama da ɗalibai miliyan 30 da ke karatu a fadin ƙasar, yana mai cewa fadar shugaban ƙasa ya kamata ta zama abin koyi wajen gaskiya, rikon amana da shugabanci nagari.

A cewar Obi, kowane ɗan Adam yana iya yin kuskure, amma abin da ke bambanta shugaba na gari shi ne yadda yake fuskantar kura-kurensa da gaskiya, ya gyara abin da ya dace, sannan ya fifita muradun ƙasa kan burinsa na siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata