Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bukaci jami’an tsaron Nijeriya, musamman sojoji, da su ƙi amincewa da karin albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi.
Obi ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, inda ya bukaci jama’ar Nijeriya da su yi watsi da shi. Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
A cewar Obi, bai taɓa cewa jami’an tsaro su ƙi karin albashin da aka amince musu da shi ba, ko kuma su jira sai bayan zaɓen 2027 kafin su karɓi karin.
Ya ce mutuncinsa da girmamawarsa ga jami’an tsaron ƙasar ba su taɓa sauyawa ba, yana mai cewa ya daɗe yana kira ga gwamnati da ta samar wa jami’an tsaro isassun kayan aiki, kulawa da kariya domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Rahoton ya zo ne bayan Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin albashi tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100 ga jami’an rundunonin sojin Nijeriya, wanda ake sa ran zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba 2026.
Karin albashin zai shafi kusan jami’an tsaro 250,000, yayin da kudin albashin shekara-shekara na rundunonin sojin Nijeriya zai tashi daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924, a cewar mai ba shugaban lasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga.
Obi ya kuma bayyana cewa damuwarsa kan walwala da tsaron sojoji ta samo asali ne daga wasu lokutan da jami’an tsaro suka rasa rayukansu yayin gudanar da ayyukan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.
Ya ce abin da ya fi damunsa shi ne yadda ake barin jami’an da ke kare ƙasa cikin yanayi mai haɗari ba tare da samun isasshiyar kariya da agajin gaggawa ba.
Obi ya ƙara da cewa, idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa, walwala, tsaro, kayan aiki da martabar jami’an tsaron Nijeriya za su kasance cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko.
Ya jaddada cewa jami’an da ke kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar sun cancanci cikakken goyon baya da kulawa daga gwamnati, yana mai cewa ba za a bar sojoji cikin mawuyacin hali ba tare da kariya ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
