Ƙasar Qatar ta bada tallafin dala dubu 50 don gina wa ƴan gudun Hijira makaranta a sansaninsu na Wassa da ke Abuja.
Jakadan ƙasar a Nijeriya Mubarak Almuhannadi ya bada gudunmuwar, ranar Talata a Abuja, lokacin da babban Kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun Hijira ta Nijeriya Sanata Basheer Muhammad suka kai masa ziyara.
Almuhannadi, ya ce dalilin bada gudunmuwar shi ne don taimakon ayyukan hukumar, na tallafa wa ƴan gudun hijirar.
A na sa ɓangaren, shugaban hukumar ya godewa ƙasar kan wannan tallafi, tare da bada tabbacin hukumar na yin amfani da kuɗin a bisa amana.
