Home Addini RA’AYI: Sai Sarkin Musulmin Nijeriya ya sauya tsarin ganin wata- Ali Sani...

RA’AYI: Sai Sarkin Musulmin Nijeriya ya sauya tsarin ganin wata- Ali Sani Madaki

326
0

Tsohon Dan Majalisar Tarayya wanda ya wakilci Karamar Hukumar Dala da ke jihar Kano Hon Aliyu Sani Madakin Gini ya yi wani ɗan tsokaci game da umarnin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’aad Abubakar ya bayar ga al’ummar Musulmin Nijeriya da su ci gaba da azumi sakamakon rashin ganin watan Shawwal.

Aliyu Madaki wanda ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta na Facebook ya ce, “maganar gaskiya harkar ganin watan mu akwai gyara. Bai kamata a ce mun ajiye sunnar Manzon Allah (SAW) mun bi maganar wani yaro a Riyadh, wanda addinin ma bai dame shi ba.”

“ya kamata Sarkin Musulmi da maluman mu su canja tunani a kan harkar ganin wata a kasarmu.” inji tsohon dan majalisar

Aliyu Sani Madakin Gini ya ce yana zullumin idan Sarkin Musulmi bai gyara tsarin ganin wata ba, gaba kadan za a iya daina biyayya ga umarninsa ka akan harkar addini.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply