Home Labarai Rage albashin da muka yi na wucin-gadi ne – Gwamnatin Kano

Rage albashin da muka yi na wucin-gadi ne – Gwamnatin Kano

249
0

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da biyan mafi karancin albashi na ₦30,000 ga ma’aikatanta.

Ta kuma bayyana cewa zaftare albashin ma’aikatan, na watan Nuwamba da Disamba na wucin gadi ne sakamakon ragi da aka samu cikin kason da gwamnatin tarayya ke ba jihar da kuma tasgaro da aka samu cikin kudin shiga da jihar ke tattarawa wanda dawowar cutar coronavirus ya haddasa.

Kwamishinan yaɗa Labarai na jihar Muhammad Garba wanda ya shaida hakan a jiya, ya bayyana cewa zaftare albashin ma’aikatan ya zama dole ne sakamakon mawuyacin halin matsin tattalin arziki da ke yi wa kasar barazana.

Ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin hakan ne a maimakon biyan rabin albashi ko kuma biyan ma’aikatan bi-da-bi kamar yadda wasu jihohin kasar ke yi.

Malam Garba ya kuma bayyana cewa irin hakan ce ta faru ga wadanda aka nada mukaman siyasa a jihar yayin bullar cutar Covid-19 a karo na farko tsakanin watan Maris da Yulin shekarar da ta gabata wanda bayan daidaitar komai aka ci gaba da biyansu kamar yadda aka saba.

Don haka, kwamishinan ya tabbatar da cewa da komai ya daidaita gwamnatin jihar za ta ci gaba da biyan ma’aikatan cikakken albashinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply