Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Rage harajin shigo da motoci Nijeriya, kashe sana’armu ne – masu ƙera...

Rage harajin shigo da motoci Nijeriya, kashe sana’armu ne – masu ƙera motoci

52
0

An bayyana amincewar gwamnatin tarayya ga rage kudin harajin shigo da motoci Nijeriya a cikin dokar kudi ta shekarar 2020, a matsayin wani yinkuri na durkusar da kasuwar kera motocin kasar.

Kamfanonin kera motoci na Nijeriya da kamfanin PAN Nigeria Limited suka bayyana wannan damuwa a wani taron ‘yan jarida da aka gudanar a Abuja.

Shugaban kamfanin PAN Ahmed Wadada Aliyu ya bayyana cewa an shammaci Ministar kudin kasar Zainab Ahmed da kididdigar da ba daidai ba, wadda ta kai ga daukar matakin.

Ya ce wannan mataki babban ci baya ne da zai iya kai wa ga rushewa kasuwar kera motoci a Nijeriya, wanda hakan zai sanya sauran kasashen Afirka ta yamma zama cibiyar kera motoci a nahiyar ba tare da Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply