Home Labarai Rage kasafin kuɗin 2020 ya zama wajibi – Majalisar Dattawa

Rage kasafin kuɗin 2020 ya zama wajibi – Majalisar Dattawa

127
0

Majalisar dattawa ta ce ba yadda za a kaucewa rage kasafin kudin Nijeriya na bana daga Naira Tiriliyan 10 da rabi, duba da yadda farashin danyan mai ya yi mummunar faduwa.


Saidai kuma majalisar ta ce hanyoyin da za a bi na rage kasafin kudin, dole ne ya zama wadanda dukkan bangarorin majalisar da na zartaswa sun amince da su.
Wannan mataki dai ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin kudi, tsare-tsare da kasafi, da kuma man fetur ya gabatar ranar Talata.

An kafa shi ne kan bukatar da ke akwai na bin diddikin illar da cutar coronavirus ta yiwa tattalin arziki da ya kai ga faduwar farashin man
An kafa kwamitin ne a makon da ya gabata karkashin jagorancin Sanata Solomon Adeola.

Inda ya gana da masu ruwa da tsaki a bangaren zartaswa da ‘yan kasuwa domin bada shawarwar da mafita kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Da yake karanta binciken kwamitin, Sanatan, ya ce za a fara dandana illar faduwar farashin man ne daga watannin Mayu, Juni da kuma Yuli.

A kan haka rahoton ya ce babu yadda za a kaucewa rage adadin kasafin kudin, saidai a tabbatar an samu amincewa tsakanin bangarorin da abun ya shafa wajen hanyoyin da za a bi na rage shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply