Home Sabon Labari RAI BAKON DUNIYA: Wasu boyayyen bayanai dangane da Dakta Junaidu Mohammed

RAI BAKON DUNIYA: Wasu boyayyen bayanai dangane da Dakta Junaidu Mohammed

35
0

Dakta Junaidu Mohammed dai kwararren likita ne amma binciken DCL Hausa ya nuna cewa marigayin ya duba wasu abubuwa na siyasa da suka wakana  a zamanin marigayi Aminu Kano a shekarun 1970 daga nan ne Dakta Junaidu ya ajiye aikin likitanci ya bi jirgin siyasar Aminu Kano har daga bisani ya zama dan majalisar wakilai a Jumhuriya ta biyu.

A cikin shekarun da ya yi ana damawa da shi a siyasar Nijeriya ya samu shaidar cewa hatta wadanda ba sa siyasa daya sun gamsu cewa Dakta Junaidu yana da ilimin abubuwan da ke gudana kuma ya san yadda zai bayyana ra’ayinsa don jama’a ta fahimci abin da ke kokon zuciyarsa.

Jaridar The Cable ta wallafa wata hira da gogaggen dan siyasar Nijeriyar a ranar 23.01.2020, inda yake cewa ya yi sa’a duk da cewa bai tara kudi ba amma yana cikin rufin asiri domin akwai wasu abokanansa da kannensa da ke daukar nauyinsa da iyalansa.

DCL Hausa na ci gaba da samun rahotannin da ke nuna cewa fitaccen dan majalisar Jamhuriya ta biyun a Najeriya ya ya rasu. Majiyioyin da suka sanar da hakan kawo yanzu akwai Yasir Ramadan Gwale da ya yi ta’aziyya a shafinsa na Facebook da kuma jaridar saheliantimes wace ake wallafawa a shafin intanet sai kuma Bashir Ahmad da ke bai wa shugaban Nijeriya shawara ta fuskar shafukan sada zumunta, wanda shi ma ya yi ta’azziya a kan mutuwar Dakta Junaidun. Jaridar Kano Focus ta ce tsohuwan dan majalisar ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply