Home Sabon Labari Ranar Ma’aikata ta bana ba ta yi armashi ba

Ranar Ma’aikata ta bana ba ta yi armashi ba

100
0

Juma’ar nan ta kasance daya ga watan Mayu, ranar ma’aikata a duniya bakidaya, inda ma’aikata a Nijeriya suka bi sahun na duniya wajen gudanar da bikin, sai dai ba cikin armashi ba wato LOW KEY, saboda yanayin cutar kwaronabairos da ake ciki, ga tsoron kada a rage ma’aikata daga aiki sakamakon durkusher tattalin arziki saboda cutar, wasu watansu na hudu ke nan ba albashi, wasu wata na biyu shiru, wasu gwamnoninsu sun yanke musu albashin da sunan gudunmawarsu ga cutar kwaronabairos, wasu fiye da shekara daya suna jiran ariyas. Da dai sauran dinbin matsaloli da ma’aikaci ke ta dambe da su a Nijeriya.

Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa Ayuba Waba ya yi gargadin ba za su yarda da kwashe albashin ma’aikata ko kokarin raba su da aikin saboda kwaronabairos ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari jinjina wa ma’aikata ya yi saboda jajircewarsu a wannan yanayi da aka shiga, tare da ba su tabbacin ba za a sallami wani ma’aikaci ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply