Mawakin jam’iyyar APC Dauda Kahutu Rarara ya ce gwada ƙwanji ne ya sa ya ce talakawa masoya Buhari su tura masa Naira dubu-dubu domin ya yi wa Shugaban waƙa, ta yadda za a gane cewa har yanzu tauraruwar shugaba Buhari na ci gaba da haskawa a ƙasar.
Rarara ya bayyana hakan ne cikin wata fira da gidan rediyon DW hausa ya yi da shi ta kafar sadarwar Instagram.
Cikin zantawar Dauda Rarara ya ce wakar6 da zai yi za ta kasance mai dogon zango, hakan ya sa zai kasafta ta kashi-kashi, inda a kashin farko zai zayyano ayyukan da shugaba Buhari ya kammala guda 192, sannan kashi na biyu zai lissafa ayyukan da aka fara sa ɗanba, sai kuma kashi na ƙarshe ya bayyana ayyukan da gwamnatin Buharin ta ƙudiri aniyar yi nan gaba.
