Wasu ‘yan Nijeriya masoya shugaban kasar Muhammad Buhari, sun fara ba da gudunmuwar kudi ga mawaki Rarara kamar yadda ya nema.

Rarara, a cikin wata ganawa da aka yi da shi, ya ce ba zai kara yi wa shugaba Buhari waka ba, har sai masoyansa na asali sun tattara masa kudi, akalla Naira dubu 1.
Wannan sako na mawakin ya haifar da cece-kuce a kafafen sadarwar zamani na “social media” da ma majalisun matasa.

To sai dai, bayan ba da bayanan asusun ajiya na banki, Rarara ya fara samun wasu daga cikin ‘yan Nijeriya sun fara ba da ta su gudunmuwa domin a ci gaba da yi wa shugaba Buhari waka kan shugabancin nagari da yake wa Nijeriya, duk daruruwan mutane da ke kokawa da matsalar talauci da rashin tsaro a sassa daban daban na kasar.
