Home Kasashen Ketare Rasha ta samar da rigakafin cutar corona

Rasha ta samar da rigakafin cutar corona

166
0

Shugaban Russia Vladmir Putin ya sanar da cewa ƙasar ta fitar da rigakafi na farko a duniya na annobar cutar korona.

Duk da rashin amincewar masana kiwon lafiya da kuma gargaɗi daga Hukumar Lafiya ta Duniya a bi a hankali, ministan lafiya Mikhail Murashko ya bayyana cewa maganin an “tabbatar yana da tasiri da aminci”.

BBC Hausa ta rawaito cewa ministan ya ƙara da cewa za a ci gaba da gwada maganin a kan daruruwan mutane.

Putin ya ce ‘yarsa daya ta yi amfani da maganin kuma ta warke daga ƙaruwar zazzaɓin da ta yi fama da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply