Home Labarai Rashin ɗaukar shawararmu ya sa tattalin arziƙin Najeriya ya sake karyewa –...

Rashin ɗaukar shawararmu ya sa tattalin arziƙin Najeriya ya sake karyewa – Atiku

132
0

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, ya nuna ɓacin ransa sakamakon yadda Nijeriya ta ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi.

A wani saƙo da Atikun ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa da a ce gwamnatin Nijeriya ta ji irin shawarwarin da ya bayar da wasu shawarwarin masu kishin ƙasa, da tuni an guje wa faruwar hakan.

Ya bayyana cewa ya bayar da shawarar Nijeriya ta rage kuɗin da take kashewa wurin gudanar da mulki, da kuma tattalin kuɗin da ta rage kashewa domin guje wa ɓacin rana, haka kuma ya ce ya ba gwamnatin shawara da ta guji ciwo bashi.

A ranar Asabar ne dai Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce tattalin arziƙin ƙasar ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, wanda hakan ke nufin tattalin arziƙin ƙasar ya samu karaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply