Home Labarai Rashin haɗin kai annoba ne ga ƙasa – Abdusalami Abubakar

Rashin haɗin kai annoba ne ga ƙasa – Abdusalami Abubakar

23
0

Tsohon shugaban Kasar Nijeriya Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga ‘yan kasar su guji abun da zai janyo rabuwar kawuna ko haddasa rikici a Nijeriya.

Tsohon shugaban na mulikin soji wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da ‘yanjarida a gidansa da ke Minna jihar Neja, ranar Talatar nan, ya ce rashin hadin kai ba karamar illa yake da ita ba ga kasa.

Abdulsalami ya bayyana damuwarsa kan ci gaba da samun tada zaune tsayen da ake yi a kasar.

Ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa don magance matsalar da ake fuskanta na rashin hadin kai, fargaba da kuma rashin kishin kasa.

Tsohon shugaban ya ce bai kamata ‘yan Nijeriya su bari makiyan kasar su yi amfani da tsoro da fargabar da ke tsakaninsu ba, wajen haddasa rikici a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply