Abdullahi Garba Jani
Wani malamin addinin musulunci Sheikh Abdurrahman Ahmad ya ce rashin hakuri ne babbar matsalar da ke yawan kawo mace-macen aure a Nijeriya.
Sheikh Abdurrahman ya yi wannan furucin ne a birnin Ibadan, inda ya ce yawan mace-macen aure na faruwa a tsakanin ma’aurata ne ta dalilin rashin hakuri da juna.
Shehin malamin ya ce aure na da bukatar hakuri da juna da kuma adu’o’i.
Sai ya shawarci ma”aurata da a kodayaushe su kasance masu hakuri da juna domin aurensu ya yi karko.
Shehin malamin ya ce dorewar aure na iya ta’allaka da yanayin mutuntaka ta gidan iyaye da kuma al’ummar da ake zaune ciki.
