Ana ci gaba da samun takaddama a cikin Jam’iyyar APC a Jihar Katsina, sakamakon rahotannin rashin jituwar siyasa tsakanin gwamnan jihar, Dikko Umar Radda, da mai ba shugaban Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari.
Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito cewa an gayyaci jami’an tsaron Gwamna Radda biyu, wato ADC dinsa, SP Abdulganiyu Bello, da Babban Jami’in Tsaronsa, DSP Hassan Bello, zuwa hedikwatar rundunar ƴan sandan Nijeriya da ke Abuja domin yi musu tambayoyi kan zargin lalata allunan tallan siyasa da ke dauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ibrahim Masari a Katsina.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, CSP Anietie Iniedu, ya musanta rahotannin da ke cewa an kama ko tsare jami’an biyu, yana mai cewa gayyatarsu kawai aka yi domin tattaunawa.
Rahotannin sun ce lamarin ya kara jawo ce-ce-ku-ce a cikin APC ta Katsina, musamman bayan ba a ga sunan Gwamna Radda da wasu na kusa da shi cikin jerin mambobin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubu na 2027 ba.
Masari na daga cikin ’yan siyasar Katsina da ake ganin suna da kusanci da Shugaba Tinubu. Ana kuma danganta takaddamar da bambancin ra’ayi tsakanin bangaren ’yan APC da ke Katsina da kuma wasu ’yan siyasar jihar da ke rike da mukamai a Abuja.
Sai dai wasu jami’an gwamnatin Katsina sun musanta cewa akwai wata babbar baraka tsakanin Gwamna Radda da fadar shugaban kasa ko tsakanin Radda da Masari.
Mai ba Gwamna Radda shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, ya ce abin da ke faruwa ba rikici ba ne, illa dai dabarun siyasa gabanin zaben 2027. Shi ma daraktan yada labarai na Gwamna Radda, Maiwada Danmalam, ya ce bai da masaniyar wata takaddama tsakanin gwamnan da Malam Ibrahim Kabir Masari.
Masu sharhi kan siyasa kuwa sun ce idan rashin jituwar ta wanzu kuma ta ci gaba, tana iya yin illa ga hadin kan APC a Katsina da kuma shirye-shiryen jam’iyyar na tunkarar zaben 2027.
