Home Labarai Rashin kunya ne tallar maganin gargajiya da kalaman batsa – Ganduje

Rashin kunya ne tallar maganin gargajiya da kalaman batsa – Ganduje

167
0

Gwamnatin Kano ta ce za ta fara kama masu tallar maganin gargajiya da ke amfani da kalaman batsa wajen tallan magungunansu.

Jaridar Solace Base ta ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje za ta fara kamen ne daga makon gobe da nufin tsabtace harkar.

Shugaban kwamitin da aka dora wa alhakin aikin, kwamishinan lafiya na jihar Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce za su yi wannan aiki ne tare da ‘yansanda da jami’ian KAROTA da ‘yan Hisbah don kamawa tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifi gaban kuliya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply