Home Labarai Rashin tsaro – Ƴanbindiga sun kori mutane daga gidajensu a Katsina

Rashin tsaro – Ƴanbindiga sun kori mutane daga gidajensu a Katsina

242
0

Wasu ƴanbindiga da yawansu ya kai 18 sun kai hari a yankin Gatakawa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Ƴanbindigar sun kai harin ne a kwanaki 2 da suka gabata cikin dare suka kone wani gida tare da kashe makwabcin mai gidan a kauyen Tabkin Gungume, sannan suka tsallaka zuwa kauyen Cediya inda nan ma suka kashe magidanci tare da sa ma gidaje sama da 8 wuta tare da runbunan hatsi.

Daya daga cikin mazauna garin ya tabbatar da faruwar lamarin ga DCL Hausa, inda ya bayyana cewa suma Allah ne ya tsaresu suka sha da kyar bayan kone gidajensu da dabbobinsu da maharan suka yi.

Shima wani da matsalar ta ritsa da shi, ya shaida wa wakilinmu cewa ba abinda ya yi saura mishi face kayan dake jikinshi, sakamakon kone gidanshi da rumbun hatsin abincinshi da aka yi, wanda ya bayyana hakan a matsayin wani mataki na tsananin rayuwa da aka jefa su da sauran mutanen yankin da ibtila’in ya afka mawa.

Ya zuwa yanzu ba kowa a garin face yan tsiraru daga cikin matasan garin, inda mata da kananan yara duk sun fice daga garuruwan don tserar da rayuwarsu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bamu samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ba, sakamakon rashin ɗaukar waya ko kuma bada amsa ga saƙon da muka tura masa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply