A ƙoƙarin ta na magance matsalar tsaron da ke ƙara taɓarɓarewa a gabacin jihar, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri ya hana yawo da babura a ƙananan hukumomi huɗu na gabacin jihar.
Dokar hana yawon dai za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ƙananan hukumomin Isa, Rabah, Goronyo da Sabon Birni.
Baya ga haka, wajibi ne masu hawa babura a ya kunan su yi rajista don tantance yawan su a faɗin yankin.
Wannan mataki dai na zuwa ne, bayan wata tattaunawa da aka yi da yammacin ranar Laraba a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 tare da hakiman waɗannan ƙananan hukumomi da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
