Home Labarai Rashin tsaro: Majalisar dattawa ta gayyaci shugabannin tsaron Nijeriya

Rashin tsaro: Majalisar dattawa ta gayyaci shugabannin tsaron Nijeriya

127
0

Majalisar dattawan Nijeriya ta gayyaci ministan tsaro da manyan hafsoshin tsaron kasar tare da shugabannin rundunar ‘yansanda da kuma na hukumar tsaron farin kaya, kan matsalar tsaron kasar da ta ki ci ta ki cinye wa.

Kiran ya biyo bayan wani kudiri da Sanata Bello Mandiya daga jihar Katsina ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata, biyo bayan sace wasu dalibai sama da 300 da aka yi a Katsina.

Majalisar ta kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta aiwatar da rahoton da ta aike masa kan matsalolin tsaron.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply