Home Labarai Rashin Tsaro: Monguno ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa Katsina

Rashin Tsaro: Monguno ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa Katsina

110
0

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno, ya jagoranci wata tawagar manyan jami’an tsaro zuwa jihar Katsina a ranar Laraba, kwana guda bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihar.

Daga cikin tawagar akwai babban Daraktan hukumar tsaron farin kaya DSS Yusuf Magaji Bichi, Babban Sufeton ‘yan sanda Muhammed Adamu, manyan jami’an ‘yan sanda da dai sauran su.

Ko da saukar su a filin jirgin Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina, tawagar ta nufi gidan gwamnatin jihar, inda suka shiga wani taron sirri da gwamna Aminu Bello Masari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply