Home Kasashen Ketare Red Cross ta yi gargaɗin ɓarkewar yunwa a yankin Tigray

Red Cross ta yi gargaɗin ɓarkewar yunwa a yankin Tigray

39
0

Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ya yi kiran samun karin tallafi domin isa ga wadanda yakin yankin Tigray na kasar Habasha ya rutsa da su.

Francesco Rocca, ya ce ya damu matuka da halin da yankin ke ciki tare da yin gargadin cewa za a fuskanci yunwa a yankin.

Ana dai sukar gwamnatin kasar kan hana kungiyoyin agaji shiga inda ake rikicin duk kuwa da alkawarin da ta yi na yin hakan.

Bayan ziyartar Birnin Mekelle, shugaban na Red Cross, ya ce yara kanana, iyaye mata da tsaffi ne suka fi bukatar taimako.

Rocca ya ce babu ko kananun magunguna a asibitoci da kuma fuskantar barazanar karancin abinci mai gina jiki.

Ya ce har yanzu ba a barin kayan agaji su isa kusan kashi 80 na yankin na Tigray.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply