Home Coronavirus Rigakafin Covid-19 miliyan 10 Nijeriya za ta samu – Minista

Rigakafin Covid-19 miliyan 10 Nijeriya za ta samu – Minista

40
0

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta samu rigakafin coronavirus Miliyan 10 nan da watan Maris.

Bayanin hakan da ya fita a cikin wata sanarwa da Ministan ya fitar ta ce wannan kari ne ga dubu 100 da ake sa ran samu daga kamfanin Pfizer.

saidai kuma sanarwar ba ta fayyace hakikanin nau’in rigakafin da ake sa ran samu ba wanda ya kai miliyan goman.

Haka kuma babu wani karin bayani kan yadda aka samar da rigakafin, walau ta hanyar Kungiyar Tarayyar Afirka ne ko kuma ta shirin COVAX, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ke hadin guiwa da kamfanoni wajen samar da rigakafin.

Nijeriya dai kasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka mai mutane kimanin miliyan 200, ta samu kimanin mutum 105, 478 da suka kamu da cutar Covid-19, kuma daga ciki 1, 405 sun mutu.

Saidai kuma ana tunanin wannan adadi da hukumomi ke fitar wa, bai kai hakikanin yawan wadanda suka kamu da cutar ba a kasar, saboda karancin gwajin cutar da ake da shi a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply